Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Kano NDLEA ta ce ta kama mutane 1,345 da wasu muggan kwayoyi a shekarar 2024

-

 

Jami’an hukumar NDLEA

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA reshen jihar Kano ta ce ta kama mutane 1,345 da ake zargi da kuma kama wasu haramtattun kwayoyi masu nauyin kilogiram dubu 8.430.239 a shekarar 2024.

Kwamandan hukumar Abubakar Idris Ahmad ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN a Kano.

Ya ce wadanda ake zargin sun hada da maza 1,301 da mata 44, ya kara da cewa haramtattun abubuwan da aka kama sun hada da hodar iblis, magungunan tari, da allurar tramadol na sama miliyan biyar.

A cewarsa, a kokarin da suke na hana shan kwayoyi a jihar Kano, sun kaddamar da ‘Operation Hana Maye’ da nufin yaki da shaye shayen miyagun kwayoyi da kuma samar da yanayi mai kyau ga al’ummar jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara