DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Nijeriya da Nijar za su ci gaba fatattakar Lakurawa duk da rikicin diflomasiyar da ke tsakaninsu

-

Chief of Army Staff

Hedkwatar tsaron Nijeriya ta jaddada aniyar ta na ci gaba da hadin gwiwa da sintiri tare da sojojin Nijar don fatattakar Lakurawa duk da zargin da shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdourahmane Tchiani ya yi wa Nijeriya.

Kamar yadda jaridar PUNCH ta rawaito wannan na daga cikin abinda da gwamnatin Nijeriya ta sa gaba na kawo karshen ayyukan kungiyoyin ‘yan ta’adda kamar Lakurawa a yankin Arewa maso Yamma da wasu sassan jihohin da ke da makwaftaka da Nijar. 

A baya bayan nan Tchiani ya zargi Nijeriya da kyale Faransa ta yi amfani da yankinta a matsayin matattarar hargitsa kasarsa.

Ya kuma yi zargin cewa gwamnatin Faransa ta bai wa Nijeriya wasu kudade domin ta kafa sansanin soji a jihar Borno.

Sai dai a martanin da mai baiwa shugaban Nijeriya shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya mayar ya yi watsi da zargin,inda ya ce zargin baya da tushe domin ko a tarihi Nijeriya ba ta ba karbar sansanonin sojojin kasashen waje ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 kudin ritayarsu

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya kudin fanshon fiye da Naira biliyan 15 ga tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 Wadanda abin ya...

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da ‘ya’yanta ke yi

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da 'ya'yanta ke yi nan da makon gobe Kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP tare da kungiyar gwamnonin...

Mafi Shahara