Tsoma baki da manyan arewa ke yi wajen tsayar da ɗan takara ci baya ne ga dimukradiyya – Kwankwaso

-

Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya zargi wasu mutane da yace na ayyana kan su a matsayin jagororin arewa da yin katsalandan a sha’anin zaben dan takarar shugabancin kasa.
A zantawarsa da BBC Hausa, jagoran darikar Kwankwasiyya, ya yi zargin cewa hakan na kawo ci baya ga dimukradiyyar kasar tare da raba kan al’umma har ta kai ga an zabi dan takarar da bai cancanta ba.
Kwankwaso kuma tsohon gwamnan Kano ya jaddada bukatar jagororin su dauki darasi daga abubuwan da suka faru a baya tare da tsame bakinsu a duk wani sha’ani na zaben dan takara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara