Firaministan kasar Senegal Ousmane Sanko, ya caccaki shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, bisa kalaman sa na cewar kasar na bada kariya ga kasashen Afirka.
Wannan dai na a cikin wani sako da Firaministan ya wallafa a shafin sa na Facebook, Ousmane Sanko ya caccaki kasar Faransa da kawo rikice-rikice da dama maimakon cigaban a nahiyar.
Ya kuma zargi Faransa da waragaza kasar Libya wanda hakan ya haddasa tabarbarewar kalubalen tsaro a yankin Sahel.
A baya bayan an alakanta koma bayan karfin ikon da Faransa ke dashi a yankin yammacin Afirka bisa rashin adalci da kulla kakkarfar alaka da kasar Rasha.