Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya yi kira ga shugaba Tinubu ya dubi halin da ‘yan Nijeriya ke ciki domin al’ummar kasar na shan wahala

-

 

Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad

Gwamnan jihar Bauchi ya yi kira ga shugaba Bola Tinubu da ya saurari halin da ‘yan Nijeriya ke ciki, da ya ce manufofinsa ba sa aiki kuma mutane suna shan wahala.

Da yake jawabi a lokacin da ya karbi bakuncin malaman addinin musulunci karkashin jagorancin Sheikh Sani Yahaya Jingir, gwamnan ya shawarci shugaban kasa da ya saurari ‘yan kasar ya  kuma gyara kura kurai da ya yi.

Ya ce ya zama wajibi shugabanni su gaya wa kansu gaskiya yana fadar hakanne domin shugaban kasa ya gyara kuskurensa domin ’yan kasar suna shan wahala da  su kansu gwamnoni  suna shan wahala saboda tsauraran  manufofin shugaban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara