DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shugaban Bola Tinubu ya sauka abirnin Abu Dhabi na kasar Dubai domin halartar taro

-

 

Shugaba Tinubu

Zuwan shugaba Tinubu zuwa Dubai na zuwa ne bisa gayyatar shugaban kasar, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan.

Mataimaki na musamman ga shugaban Tinubu kan kafafen sadarwa na zamani, Dada Olusegun, ya sanar da hakan Tinubu a shafin sa na X.

Shugaba Bola Tinubu ya gana da karamin ministan harkokin wajen kasar, Sheikh Shakhboot Nahyan Al Nahyan, a lokacin da ya sauka a birnin Abu Dhabi a ranar 12 ga watan Junairu, 2025. A Abu Dhabi.

Ana sa ran shugaban zai gabatar da jawabin da zai bayyana sauye sauyen da gwamnatinsa ta kawo ga Nijeriya, musamman inganta harkokin sufuri, lafiyar al’umma, da ci gaban tattalin arziki.

A yayin ziyarar, Tinubu da tawagarsa za su tattauna da shugabannin kasar don karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma lalubo damammaki na huldar tattalin arziki da diflomasiyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 kudin ritayarsu

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya kudin fanshon fiye da Naira biliyan 15 ga tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 Wadanda abin ya...

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da ‘ya’yanta ke yi

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da 'ya'yanta ke yi nan da makon gobe Kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP tare da kungiyar gwamnonin...

Mafi Shahara