Hukumar kula da shige da fice “Immigration” ta tseratar da mutanen da aka yi yunkurin safararsu a Jigawa

-

Hukumar lura da shige da fice ta Najeriya Immigration a jihar Jigawa ta kubutar da mutum 10 da ake zargin an yi safarar su ya yin wani samame da ta kai a karamar hukumar Babura.
Shugaban hukumar a jihar CIS Musa ne , ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema Labarai a ofishin sa dake birnin Dutse.
Ya ce bayan samamen da aka kai mai taken ‘Operation Salama’ a Naira Tsamiyar Kwance a Babura, an kubutar da Mata 8 sai Maza biyu da ke kan hanyar zuwa Turai.
CIS Musa, ya ce wadan da aka yi safarar su matasa ne da shekarun su ke tsakanin 21 zuwa 30, kuma sun fito ne daga jihohin Ogun sai Oyo da Ondo da kuma Imo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara