DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shirin ba da bashin karatu ga daliban Nijeriya ba ya da tabbas – Kungiyar ASUU

-

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya ASUU, ta ce bai kamata bashin da ake bawa dalibai na Karatu NELFUND, ya maye gurbin aiyyukan asusun tallafawa manyan makarantu TETFUND ba.
Kungiyar ta ce zata yi duk mai yiwuwa don ganin cewar ba a kassara ko dakile aiyyukan TETfund ba duba da gagarumin aikin da take na bunkasa fannin Ilimi a Najeriya, tun bayan kafa ta a shekarar 2011.
ASUU tace tsarin bashin kudin karatu wasu ‘yan tsirarin dalibai kawai zai amfana sabanin wanda yake taimakawa dukkanin makarantun gaba da Sakandire na Najeriya a karkashin TETfund.
Da yake karin haske kan matsayar ta ASUU, shugaban kungiyar shiyyar Nsukka dake jihar Enugu Raphael Amokaha, yace fito da wasu tsare -tsare dangane da tallafawa Ilimi dai dai yake da kassara aiyyukan TETfund, don haka ba zasu lamunta ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 kudin ritayarsu

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya kudin fanshon fiye da Naira biliyan 15 ga tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 Wadanda abin ya...

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da ‘ya’yanta ke yi

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da 'ya'yanta ke yi nan da makon gobe Kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP tare da kungiyar gwamnonin...

Mafi Shahara