Shugaba Tinubu ya umarci da a mayar da wadan da suka jikkata sakamakon fashewar tankar mai a jihar Neja zuwa manyan cibiyoyin kiwon lafiya domin ci gaba da basu kulawa ta musamman

-

Shugaba Tinubu

A cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga ministan yada labarai Rabiu Ibrahim ya fitar a ranar Litinin ya ce an kwantar da marasa lafiyan guda 20 a asibitin kwararru na Gwagwalada da ke Abuja.Hakazalika an kai karin wasu mutum biyu zuwa cibiyar kiwon lafiya ta tarayya dake Jabi, Abuja.

Sanarwar ta kara da cewa dukkan marasa lafiyan suna tare da ma’aikatan jinya da ‘yan uwan su a wuraren da aka kaisu don basu kulawa ta musamman.

Lamarin fashewar tankar mai na ci gaba da yawaita a ‘yan shekarun nan, da ko a farkon watan Janairu, akalla mutane biyar ne suka rasu a lokacin da wata tankar mai dauke da man fetur ta kama da wuta a yankin Agbor na jihar Delta.

 A watan Oktoban shekarar da ta gabata ma wata tankar mai da ta fadi a jihar Jigawa ta kashe mutane sama da 170 tare da jikkata wasu da dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara