Nijeriya na da isassun kuɗin da Shugaba Tinubu zai yi tafiye-tafiye kasashen duniya – Ministan harkokin waje

-

Ministan Harkokin Wajen Nijeriya Yusuf Tuggar, ya ce Nijeriya na da isassun kuɗin da za ta iya daukar nauyin tafiye-tafiyen Shugaba Bola Tinubu zuwa kasashen ketare.

Ministan ya bayyana hakan ne a cikin shirin siyasa da gidan talabijin na Channels ke gabatarwa.

Wasu ‘yan Nijeriya dai na yin guna-guni kan yadda shugaban kasar ke yin balaguro daga kasa zuwa kasa, ba tare da kasar ta samu wani ci gaba ba.

Sai dai Ministan ya yi watsi da wannan, inda yace ziyarar shugaban ta jawo wa Nijeriya masu zuba hannun jari da suka saka dala biliyan 2 bayan ziyarar da ya kai a ƙasar Brazil.

Tun bayan hawa karagar mulki a shekarar 2023, rahotanni sun ce Shugaba Tinubu ya ziyarci kasashe kusan 19 a tafiye-tafiye 32 kasashen ketare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara