DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin Najeriya ta dakatar da kamfanin jiragen Max Air na wata uku bayan hatsarin da ya faru a Kano

-

Gwamnatin Najeriya ta dakatar da kamfanin jiragen sama na Max Air na tsawon wata uku bayan fashewar tayar jirgin a daren Talata a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, dake jihar Kano.
Da yake sanar da dakatarwar, jami’in yada labarai na hukumar lura da harkokin sufurin jirage ta Najeriya (NCAA) Micheal Achimugu, ya ce an dakatar da kamfanin na wata uku ne har sai hukumar ta NCAA ta yi kwakwaran binciken tabbatar da lafiyar jiragen kamfanin Max Air.
Lamarin na baya baya nan shi ne karo na uku cikin watanni uku da jiragen kamfanin na Max Air ke samun matsala, a cewar jaridar Dailytrust.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Farashin buhun shinkafar waje mai nauyin 50KG ya koma N58,000 a wasu sassan Nijeriya in ji wani rahoton da majiyar DCL Hausa ta Punch ta wallafa.

Rahoton da kamfanin S&P Global ya fitar ya bayyana cewa farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 ya sauka zuwa N58,000 a wasu yankunan Najeriya,...

‘Yan siyasar da ke neman mukamai ba don talakawa suke yi ba – Zargin Bafarawa ga ‘yan siyasar Nijeriya

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya yi zargin cewa an yi wa siyasar adawa kamshin mutuwa a Najeriya. Bafarawa, wanda ya kasance jigo...

Mafi Shahara