DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Najeriya ta karbi bashin sama da biliyan 1 daga bankin bunkasa kasashen Afirka AfDB

-

Najeriya ta samu sahalewar karbar bashin dala biliyan 1.1 daga bankin bunkasa kasashen Afirka AfDB don samar da wutar lantarki ga al’ummar kasar miliyan 5 zuwa karshen shekarar 2026.

Shugaba Bola Tinubu ne ya bayyana haka ta bakin ministan samar da lantarki Adebayo Adelabu ya yi a taron kwana biyu na harkokin lantarki a Afirka  da aka gudanar a birnin Dar es Salam na kasar Tanzania, kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawunsa Bayo Onanuga ya fitar ta bayyana.

Shugaban ya gode wa shugaban bankin raya kasashen Afrika Akinwunmi Adesina da na bankin duniya Ajay Banga, bisa wadannan kudaden da suka bai wa Nijeriya domin bunkasa samar da lantarki ga al’ummar kasar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An saka ranar da za a fitar da sakamakon binciken zargin alaka da muggan kwayoyi da ya hada da Shugaba Tinubu na Nijeriya

An saka ranar da za a fitar da sakamakon binciken zargin alaka da muggan kwayoyi da ya hada da Shugaba Tinubu na Nijeriya. Ana dai...

Za mu iya cin zabenmu ko babu ku, kalaman Elrufa’i ga gwamnonin Nijeriya

  Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa sabuwar kawancen jam’iyyu adawa na da karfin da zai kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu...

Mafi Shahara