An kori wasu jami’an ‘yan sanda uku bisa zargin rashawa da garkuwa da mutane

-

 

Police

Rundunar ‘yan sandan jihar Abia da ke kudu maso gabashin Nijeriya ta kori wasu jami’anta uku bisa zarginsu da rashin da’a.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Maureen Chinaka ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a.

Chinaka, ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Abia, Danladi Isa ne ya  bada umarnin korar jami’an ‘yan sandan.

Kakakin ‘yan sandan ta bayyana sunayen jami’an da aka kora da suka hada da Jonas Nnamdi,  sai James Daniel, da Ifeanyi Emeka.

A cewar ta an kori jami’an uku ne saboda dabi’u mara sa kyau da suka hada da rashawa, hada baki, da satar  mutane ta hanyar yin garkuwa dasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara