DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Babban Hafsan tsaron Nijeriya Janar Christopher Musa ya tabbatar da halaka wasu jiga jigan ‘yan bindiga guda biyu a jihar zamfara

-

CDS Christopher Musa

 

Babban hafsan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa ya tabbatar da halaka wasu jiga jigan bindiga guda biyu,da suka hada da Kachalla Gwammade da Kachalla Shehu.

CDS ya bada wannan tabbaci ne a wajen rufe taron kwamandojin hadin gwiwa a ranar Juma’a.

Majiyoyi sun bayyana cewa dakarun da ke kan hanyar Magami, Dan Sadau ne suka kai farmakin tare da hadin gwiwar ‘yan banga na yankin.

Majiyar ta tabbatar da cewa sojojin sun yi artabun ne da ‘yan bindigar da suka yi nasarar halaka guda shida tare da kwato babura uku da kuma bindigogi da dama, kuma Kachalla Gwammade da Kachalla Shehu na daga cikin su.

Kachalla Gwammade, wanda aka bayyana a matsayin babban kwamandan ‘yan bindigar, na daga cikin wani sansani a kauyen Chabi da ke karamar hukumar Maru, a jihar ta Zamfara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Farashin buhun shinkafar waje mai nauyin 50KG ya koma N58,000 a wasu sassan Nijeriya in ji wani rahoton da majiyar DCL Hausa ta Punch ta wallafa.

Rahoton da kamfanin S&P Global ya fitar ya bayyana cewa farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 ya sauka zuwa N58,000 a wasu yankunan Najeriya,...

‘Yan siyasar da ke neman mukamai ba don talakawa suke yi ba – Zargin Bafarawa ga ‘yan siyasar Nijeriya

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya yi zargin cewa an yi wa siyasar adawa kamshin mutuwa a Najeriya. Bafarawa, wanda ya kasance jigo...

Mafi Shahara