DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Likita daya ke kula da lafiyar masu lalurar “cancer” 1,800 a Nijeriya – Kungiyar masu dauke da ‘cancer ta kasa’

-

 

Shugaban kungiyar, Farfesa Abidemi Emmanuel Omonisi, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan taron tunawa da ranar cutar “Cancer” ta duniya. 

Farfesa Omonisi ya ce rashin samun isasshen albashi, da rashin tsaro, rashin tsarin kiwon lafiya ingantacce, sune suka haifar da fitar likitocin cutar “Cancer”, likitocin manyan cututtuka,da malaman jinya zuwa kasashen ketare.

Ya kara da cewa saboda karancin likitocin da ke kula da masu cutar zuwa yanzu karuwa take yi,kuma ana samun dogayen layuka asibitocin da ake kula da masu cutar ta “Cancer” a fadin kasar.

Sai dai yi kira ga shugabanni a Nijeriya da su magance abinda ke sa kwararrun ma’aikatan lafiya a kasar ke yin gudun hijira zuwa wasu kasashen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 kudin ritayarsu

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya kudin fanshon fiye da Naira biliyan 15 ga tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 Wadanda abin ya...

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da ‘ya’yanta ke yi

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da 'ya'yanta ke yi nan da makon gobe Kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP tare da kungiyar gwamnonin...

Mafi Shahara