![]() |
Shugaba Tinubu |
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa Mohammed Idris ne ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata.
Ministan ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya umurci dukkanin ministocin da su ringa neman manema labarai lokaci lokaci don bayar da bayanai kan ayyukansu da manufofin gwamnatin sa.
A cewar sa, ganawar za ta kasance wata kafa ce da ministocin za su yi hulda kai tsaye da ‘yan Nijeriya, da bayyana muhimman abubuwan da ke faruwa a ma’aikatun su, da kuma magance matsalolin al’umma.