Dan majalisar wakilai daga jihar Kebbi ya bar PDP ya koma jam’iyyar APC

-

 

Dan Majalisar wakilai mai wakiltar Besse/Maiyama daga jihar Kebbi, Salisu Garba Koko, ya bar PDP zuwa jam’iyyar APC.

Salisu Koko ya bayyana sauya shekar tasa ne a wata wasika da ya aike wa majalisar kuma kakakin majalisar, Abbas Tajudeen ya karanta.

Dan majalisar a wasikar ta sa, ya bayyana cewa ficewar ta sa baya rasa nasaba da rikicin cikin gida da ya dade yana addabar jam’iyyar PDP.

Ficewar Koko na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da wani dan jam’iyyar daga jihar Kaduna, Amos Magaji, ya fice daga babbar jam’iyyar adawa, bisa dalilin makamancin haka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara