DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shugaba Tinubu ya cancanci yin shekara 8 yana mulkin Nijeriya – Ganduje

-

 

Ganduje / Shugaba Tinubu

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya dage cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai yi wa’adi na biyu na shekaru takwas a kan karagar mulki tsakanin 2023 zuwa 2031.

Ganduje da yake maida martani kan kalaman tsohon Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-rufa’i a ranar Talata a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar matasan Arewa na Tinubu a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja, ya ci gaba da cewa ba za a sauya ka’idar mika mulki tsakanin Arewacin Nijeriya da Kudancin kasar ba don haka shugaba Tinubu zai yi shekaru takwas koda mulki zai dawo Arewa.

Gandujen ya yi tsokaci ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda yayi wa’adi biyu akan karagar mulki domin ya tabbatar da cewa shugaba Tinubu shima zai samu irin wannan gatan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Farashin buhun shinkafar waje mai nauyin 50KG ya koma N58,000 a wasu sassan Nijeriya in ji wani rahoton da majiyar DCL Hausa ta Punch ta wallafa.

Rahoton da kamfanin S&P Global ya fitar ya bayyana cewa farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 ya sauka zuwa N58,000 a wasu yankunan Najeriya,...

‘Yan siyasar da ke neman mukamai ba don talakawa suke yi ba – Zargin Bafarawa ga ‘yan siyasar Nijeriya

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya yi zargin cewa an yi wa siyasar adawa kamshin mutuwa a Najeriya. Bafarawa, wanda ya kasance jigo...

Mafi Shahara