HomeUncategorizedSojojin Nijeriya sun halaka ‘yan bindiga da dama, tare da lalata maboyarsu...

Sojojin Nijeriya sun halaka ‘yan bindiga da dama, tare da lalata maboyarsu a dajin Sakkarawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto

-

 

CDS Christopher Musa

Rundunar hadin gwiwa ta Operation FANSAR YAMMA tare da hadin gwiwar ‘yan sakai sun halaka tare da lalata wata maboyar ‘yan bindiya wadda akafi sani da “Dan Dari Biyar” da ke dajin Sakkarawa a yammacin Sabon Birni a jihar Sokoto.

Wasu majiyoyi sun tabbatarwa da mai sharhi kan al’amuran tsaro Zagazola Makama cewa an halaka wasu ‘yan bindiga a yankin yayin da wasu suka yi nasarar tserewa da munanan raunuka a harin da aka kai a ranar 17 ga Fabrairu, 2025. 

Wani wanda aka ceto daga cikin wa’yanda ‘yan bindigar sukai garkuwa da shi a kwanakin baya, bayan ya shafe watanni biyu a tsare a sansanin ‘yan bindigar, ya bayyana irin halin da ya shiga da irin wahalar da ya sha a hannun su. 

Sai dai majiyar ta ce jami’an tsaro sun zafafa kai hare hare kan ‘yan ta’addan da suka tsere tare da tabbatar da cewa sun share yankin gaba daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Sarkin Daura ya nada Hamza Sule Sarautar Sadaukin Kasar Hausa

Maimartaba Sarkin Daura Alh Faruk Umar Faruk ya nada Hon. Hamza Sulaiman Faskari Kwamishinan mahallin jihar katsina sarautar Sadaukin Kasar Hausa a fadarsa dake garin...

Kawance domin kayar da Tinubu a 2027 ba zai yi wani tasiri ba, bata lokaci ne kawai, in ji dan jam’iyyar PDP Ayo Fayose

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya yi watsi da gamayyar jam’iyyun adawa na siyasa da ake tattaunawa a kai, da nufin kifar da Gwamnatin...

Babu wanda ya hana Kasshim Shettima shiga fadar Shugaban kasa ta Villa, labarin ba ya da tushe bare makama – Mai magana da yawunsa...

Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai Stanley Nkwocha,ya bayyana labarin da ke yawo a kafafan sada zumunta, dangane da hana...

Jiga-jigan APC sun tattaru a Abuja, sun tabbatar wa da Shugaba Tinubu zai yi nasara da gagarumin rinjaye a zaben 2027

Jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulki sun gudanar da wani gangami a Abuja, inda suka bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu gagarumin rinjaye a...

Most Popular

spot_img