DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin tarayya ta bukaci ‘yan kasuwa da su rage farashin kayan abinci

-

 

Google search engine

Ministan Noma da albarkatun kasa Abubakar Kyari ne ya bayyana bukatar hakan a ranar Talata, a yayin wani bikin noman alkama da aka gudanar a kauyen Dabi dake karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa.

Ministan ya bayyana takaicinsa kan yadda wasu ‘yan kasuwa suka ki sauke farashi duk da saukowar kayayyaki, yana mai bayyana hakan a matsayin rashin kishin ƙasa.

Ya ce gwamnatin tarayya tana sane da saukar farashin kayan abinci a wasu manyan kasuwanni, musamman na kayan masarufi kamar su gari, sukari, shinkafa da taliya.

Amma duk da haka wasu, masu yin burodi, da masu shaguna a cikin Unguwanni sun ki sauke farashin kayyayyakin amfanin yau da kullum, a saboda haka ya yi kira da su sauke farashi kamar yadda yake sauka a wasu kasuwanni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Shugaba Tinubu ya yi kira da a zauna lafiya gabanin zaɓen Abuja, Kano da Rivers

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga masu kaɗa ƙuri’a, jami’an tsaro da jami’an Hukumar zaɓe Mai zaman kanta (INEC) da su gudanar...

Gwamnatin Nijeriya za ta kafa kwalejin koyon likitanci ta sojoji don magance karancin likitoci

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da shirin kafa kwalejin koyon likitanci ta soji "Armed Forces College of Medicine and Health Sciences" a matsayin wani mataki na...

Mafi Shahara