DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Idan har za a yi zabe na gaskiya, to babu shakka nine zan lashe zaben 2027 – Sanata Rabi’u Kwankwaso

-

 

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP tsagin mai littafi, ya ce jam’iyyarsa za ta kayar da jam’iyya mai mulkin Nijeriya APC da kuma babbar jam’iyyar adawa ta PDP da sauran jam’iyyu a kasar idan aka yi zaben.
Kwankwaso wanda ke jawabi a wurin taron shugabannin jam’iyyar da ya gudana a Abuja, ya yi nuni da cewa ‘yan Najeriya ba su ji dadin salon mulkin da ake yi a yanzu ba.
Yace ‘yan Nijeriya na sane da matsalolin da PDP ke fuskanta, da kuma halin da salon mulkin jam’iyyar APC ya jefa su, a saboda haka ya yabawa goyon bayan da ‘yan kasa suka bashi a zaben 2023, inda ya ba su tabbacin cewa a 2027 shine zai zama shugaban Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 kudin ritayarsu

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya kudin fanshon fiye da Naira biliyan 15 ga tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 Wadanda abin ya...

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da ‘ya’yanta ke yi

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da 'ya'yanta ke yi nan da makon gobe Kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP tare da kungiyar gwamnonin...

Mafi Shahara