DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnan jihar Plateau Mutfwang ya dakatar da hakar ma’adinai a jihar

-

Gwamnan jihar Plateau a Najeriya Caleb Mutfwang ya sanya wa wata doka hannu da ta haramta hakar ma’adinai a fadin jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a wannan Assabar 22 ga Fabrairu a fadar gwamnatin jihar.
Mutfwang yace daukar matakin dakatar da hakar ma’adinan na da nasaba da kokarin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar tare da kare muhalli da kuma kubutar da yara daga aikin karfi.
Haka zalika gwamnan ya kafa kwamitin da zai yi duba akan hakar ma’adinan ta re da bada shawarwarin sauya akalar hakar ma’adinan a jihar, karkashin jagorancin kwamishinan shari’a na jihar Barista Philemon Dafi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 kudin ritayarsu

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya kudin fanshon fiye da Naira biliyan 15 ga tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 Wadanda abin ya...

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da ‘ya’yanta ke yi

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da 'ya'yanta ke yi nan da makon gobe Kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP tare da kungiyar gwamnonin...

Mafi Shahara