DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Jam’iyyar NNPP a Kano ta dakatar da Sanata Kawu Sumaila da wasu mutane ukku

-

Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta dakatar da sanata da wasu yan majalissu na jam’iyyar mutum 4 wadanda suka hada da Sanata Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta Kudu, Alhaji Abdullahi Sani Rogo, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Rogo, Alhassan Rurum mai wakiltar Rano da Kibiya, da kuma Ali Madakin Gini mai wakiltar mazabar Dala a majalisar wakilai ta Nijeriya.

Wannan sanarwa ta fito ne daga shugaban jam’iyyar na jiha Hon. Hashim Sulaiman Dungurawa yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano.

A cewar shugabanjam’iyyar, an zabi ‘yan majalisar dokokin ne a karkashin jam’iyyar NNPP amma a baya-bayan nan an hango su sun tsunduma cikin ayyukan da suka saba wa muradun jam’iyyar tare da karya ka’idojin jam’iyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 kudin ritayarsu

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya kudin fanshon fiye da Naira biliyan 15 ga tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 Wadanda abin ya...

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da ‘ya’yanta ke yi

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da 'ya'yanta ke yi nan da makon gobe Kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP tare da kungiyar gwamnonin...

Mafi Shahara