DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Mutane miliyan uku a yankin Arewa maso yamma ne ke shan miyagun kwayoyi – NDLEA

-

 

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Nijeriya NDLEA ta bayyana cewa kimanin mutane miliyan uku a yankin Arewa maso yamma ke shan miyagun kwayoyi. 

Shugaban hukumar na kasa Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa ne ya bayyana haka a yayin wani taro da aka shirya a yankin Arewa maso yamma na yaki da shan miyagun kwayoyi a Kaduna.

Shugaban hukumar ta NDLEA ya ce gangamin wayar da kan al’umma mai taken ‘Dakatar da shaye shayen miyagun kwayoyi a cikin al’umma, wata shaida ce ta sadaukar da kai wajen kauda al’umma daga barna da ta’ammali da miyagun kwayoyi ke haifarwa.

Shugaban majalisar wakilai Tajuddeen Abbas ne ya dauki nauyin shirin wayar da kan al’umma da hukumar wayar da kan jama’a ta kasa NOA tare da hadin gwiwar hukumar NDLEA suka shirya.

Ya ce a binciken da Hukumar kula da magunguna da laifuka ta Majalisar Dinkin Duniya (UNODC) ta gudanar a shekarar 2018 ya bayyana wani lamari mai ban tsoro,cewa kusan ‘Yan Nijeriya miliyan 14.3 masu shekaru 15-64 na amfani da kwayoyin da ke kauda hankali da tunani.

Ya kara da cewa, yankin Arewa maso Yamma da ta kunshi jihohi bakwai da suka hada da Kaduna, Katsina, Kano, Jigawa, Kebbi, Zamfara da Sokoto, suna fama da matsalar shaye shayen miyagun kwayoyi, inda Kano ce tafi kowacce jiha da kashi 16 cikin 100.

Binciken ya kiyasta cewa kashi 12% na al’ummar yankin kimanin mutane miliyan uku ne ke amfani da miyagun kwayoyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Muna kokarin bunkasa tattalin arzikin Nijeriya zuwa dala tiriliyan 1 – Kashim Shettima

Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya ce gwamnatin kasar na kan hanyar bunkasa tattalin arzikin Nijeriya zuwa dala tiriliyan 1 cikin shekaru goma masu zuwa. Kashim...

Yan sanda sun dakile yunkurin garkuwa da direba da fasinjoji a Katsina

Jami’an rundunar ‘yan sandan Nijeriya sun dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane a hanyar Funtua zuwa Gusau a Katsina. Jami’an sun yi artabu da ‘yan...

Mafi Shahara