DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kungiyoyin Arsenal da Liverpool sun tuntubi Atalanta kan yuwuwar daukar dan wasa Ademola Lookman a kakar wasa mai zuwa

-

Ademola Lukman

Arsenal da Liverpool sun tuntubi Atlanta kan yiwuwar daukar dan wasan Nijeriya mai shekaru 27, Ademola Lookman daga kungiyar da ke buga Seria A, kamar yadda  thehardtackle.com ta rawaito.

A cewar wani rahoto daga Sacha Tavoleri Lookman na iya komawa gasar Premier a lokacin kakar wasa mai zuwa.  Arsenal da Liverpool na daga cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan na Atalanta bayan wata cacar baka da sukayi da Gian Piero Gasperini kan zubar da Fanareti da dan wasan ya yi a makwannin da suka gabata a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai.

Google search engine

Lookman na daya daga cikin mafi kyawun ‘yan wasa a Seria A tun lokacin da ya koma Atalanta daga RB Leipzig, a watan Agusta 2022.

Sai dai Arsenal ta bayyana sha’awarta na daukan dan wasan gaban,bisa bukatar da take da shi tun bayan da wasu daga cikin ‘yan wasan gaban ta suka samu rauni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Muna biyan ‘yan bindiga Naira miliyan 7 don zama a gidajenmu ko noma gonakinmu

Wasu al’ummomi a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja sun bayyana cewa suna biyan haraji ga ‘yan bindiga domin su samu damar zama a garuruwansu...

Abin takaici ne a ce tawagar Super Eagles na bin bashi – Peter Obi

Tsohon ɗan takarar shugaban Nijeriya na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023 Peter Obi, ya bayyana takaici kan rahotannin da ke nuna cewa tawagar wasan...

Mafi Shahara