DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Jami’an tsaro sun yi nasarar ajalin kasurgumin dan ta’addar Lakurawa da ake kira Maigemu a jihar Kebbi

-

Nasir Idris

Tawagar jami’an tsaro da suka hada da ‘yan bijilanti sun yi nasarar kawar da fitaccen dan ta’addan  Lakurawa da akafi sani da  Maigemu a jihar Kebbi.

Daraktan harkokin tsaro na jihar, AbdulRahman Usman Zagga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a a Birnin Kebbi.

Ya ce an kashe Maigemu ne a ranar Alhamis a Kuncin Baba da ke karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbi, yankin da ke fama da yan ta’addan.

Ya kara da cewa wannan ya zo ne mako guda bayan da gwamnan jihar Nasir Idris ya ziyarci al’ummar Bagiza da Rausa Kade a karamar hukumar Arewa domin jajantawa mazauna garin bisa kashe wasu mutane shida da ake zargin yan ta’addan Lakurawa ne suka yi.

A yayin ziyarar gwamnan, ya tabbatar wa al’ummomin  yankin cewa za a inganta tsaro cikin gaggawa tare da daukar matakan da suka dace don magance miyagun laifuka a yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An saka ranar da za a fitar da sakamakon binciken zargin alaka da muggan kwayoyi da ya hada da Shugaba Tinubu na Nijeriya

An saka ranar da za a fitar da sakamakon binciken zargin alaka da muggan kwayoyi da ya hada da Shugaba Tinubu na Nijeriya. Ana dai...

Za mu iya cin zabenmu ko babu ku, kalaman Elrufa’i ga gwamnonin Nijeriya

  Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa sabuwar kawancen jam’iyyu adawa na da karfin da zai kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu...

Mafi Shahara