HomeUncategorizedFitar El-Rufa'i wasu jiga-jigai a APC na shirin komawa zuwa jam'iyyar...

Fitar El-Rufa’i wasu jiga-jigai a APC na shirin komawa zuwa jam’iyyar SDP – Shugaban jam’iyyar SDP a Nijeriya Gabam

-

 

Alamu na nuna cewar  wasu manyan ‘yan siyasa sun kammala shirin komawa jam’iyyar SDP biyo bayan ficewar tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai daga jam’iyyar APC mai mulki.

Shugaban jam’iyyar SDP na kasa, Shehu Musa Gabam ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, a wata tattaunawa da yayi da gidan talabijin na Trust yayin da yake mayar da martani kan sauya shekar ta El-Rufai.

Gabam ya bayyana cewa matakin da El-Rufai ya dauka ya kawo  sauye-sauyen ficewa daga jihar Kaduna, inda ake sa ran wasu fitattun jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulki da sauran jam’iyyu da dama za su yi koyi da shi.

Wasu majiyoyi daga cikin jam’iyyar na nuni da cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi da tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, suma suna shirin koma jam’iyyar SDP.

El-Rufai dai ya ziyarci Aregbesola da wani malamin addinin kirista Fasto Tunde Bakare a Legas ranar Lahadi.

Ya kuma gana da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a kwanakin baya.

Wadannan ziyarce ziyarce sun kara rura wutar rade-radin cewa El-Rufai ya nuna mafarin sauye-sauyen sheka a siyasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Sarkin Daura ya nada Hamza Sule Sarautar Sadaukin Kasar Hausa

Maimartaba Sarkin Daura Alh Faruk Umar Faruk ya nada Hon. Hamza Sulaiman Faskari Kwamishinan mahallin jihar katsina sarautar Sadaukin Kasar Hausa a fadarsa dake garin...

Kawance domin kayar da Tinubu a 2027 ba zai yi wani tasiri ba, bata lokaci ne kawai, in ji dan jam’iyyar PDP Ayo Fayose

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya yi watsi da gamayyar jam’iyyun adawa na siyasa da ake tattaunawa a kai, da nufin kifar da Gwamnatin...

Babu wanda ya hana Kasshim Shettima shiga fadar Shugaban kasa ta Villa, labarin ba ya da tushe bare makama – Mai magana da yawunsa...

Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai Stanley Nkwocha,ya bayyana labarin da ke yawo a kafafan sada zumunta, dangane da hana...

Jiga-jigan APC sun tattaru a Abuja, sun tabbatar wa da Shugaba Tinubu zai yi nasara da gagarumin rinjaye a zaben 2027

Jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulki sun gudanar da wani gangami a Abuja, inda suka bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu gagarumin rinjaye a...

Most Popular

spot_img