![]() |
Sim Fubara |
Sa’o’i kadan bayan gwamnan jihar Rivers Similanayi Fubara ya sake mika wata bukata ga majalisar dokokin jihar ta gabatar da kudirin kasafin kudi na shekarar 2025, majalisar ta dage zaman ta har sai baba ta gani.
Dage zaman majalisar ya zo ne sa’o’i kadan bayan da gwamnan ya ce ya aika wa majalisar wasika karo na biyu domin gabatar da kasafin kudin jihar na 2025.
An cimma matsayar dage zaman har sai baba ta gani a zauren majalisar karkashin jagorancin kakakin majalisar Martins Amaewhule.
Gwamna Fubara a cikin wasikar da ya aike wa shugaban majalisar ya sanar da majalisar aniyarsa ta gabatar da kasafin kudin a ranar 19 ga Maris, 2025.
A cikin wasikar, ya bukaci majalisar ta kuma zabi duk ranar da ta dace banda ranar 19 ga Maris domin gabatar da kasafin kudin.
Bayan ya kasa cika wa’adin sa’o’i 48 da ‘yan majalisar suka ba shi, Fubara ya je harabar majalisar a ranar Laraba domin gabatar da kasafin kudin, amma an kulle kofar.
Dage zaman majalisar yazo ne a daidai lokacinda gwamnan ke kokarin sasantawa da ‘yan majalisa 27 da ke biyayya ga tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike, wanda ya gaje shi, bayan hukuncin kotun koli.