![]() |
Filin jirgin saman Maiduguri |
Shugaba Tinubu ya amince da a daga darajar filin jirgin saman Maiduguri da ke jihar Borno zuwa matsayin na kasa da kasa.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Sunday Dare ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis.
A cewar mai taimaka wa shugaban kasar, amincewar shugaban ya zone daidai lokacin da ake kokarin kafa filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa a yankuna shida na kasar.