![]() |
Gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso na shirin samar da sabbin dakaru da suka hada da sojoji dubu 14,000 da dubban ma’aikatan agaji na farar hula, domin yakar ta’addancin masu ikirarin jihadi a kasar.
Kasar Burikina Faso na fuskantar hare-haren na kungiyoyin ta’addanci a cikin shekaru 10 da suka gabata, wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojoji da fararen hula kusan 26,000,wanda ya tilastawa mutane sama da miliyan biyu barin gidajensu.