Kungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya ta musanta ikirarin da aka yi na cewa tana adawa da rage farashin man fetur da matatar Dangote da kamfanin mai na Nijeriya suka yi.
Wani mai taimaka wa tsohon shugaban kasa Reno Omokri, a wani sako da ya wallafa a shafin sa na X,a daren ranar Asabar, ya yi zargin cewa kungiyar IPMAN na adawa da gwamnatin tarayya ne saboda ragin kudin man fetur da Dangote da NNPC.
Ya rubuta cewa, a karon farko a tarihin Nijeriya,kungiyar ‘yan kasuwar man fetur IPMAN, suna nuna adawa da gwamnatin Nijeriya saboda man fetur din NNPC da na matatar Dangote yana da arha har man da suke shigo da su ke janyo musu asarar kudi.