![]() |
‘Yan sanda |
Jami’an tsaro sun dakile wani hari da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai a karamar hukumar Danmusa da ke jihar Katsina.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
Ya ce aikin da aka yi a ranar Asabar din da ta gabata ya kasance tare da hadin gwiwar ma’aikatar ayyuka ta jihar, da kuma ‘yan kungiyar sa kai ta jihar Katsina.
A cewarsa, ‘yan bindigar sun yi yunkurin kai hari kauyen Dan Takuri na karamar hukumar Danmusa da ke jihar.
A ranar 15 ga Maris, 2025, bayanan sirri da aka samu daga jami’an tsaro na farin kaya a Danmusa, ‘yan bindigar masu tarin yawa sun hau tsaunin Maijele da ke karamar hukumar Danmusa a yunkurin kai hari kauyen Dan Takuri.
Bayan samun labarin, ba tare da bata lokaci ba, tawagar hadin guiwar jami’an ‘yan sanda da ‘yan karkashin jagorancin DPO Danmusa suka afkawa tsaunin da ake zargin ‘yan fashin ne suke taruwa.