![]() |
Godswill Akpabio |
Kungiyar SERAP mai fafutikar yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya ta yi karar shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, kan kin sauya matakin dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha Akpoti ba bisa ka’ida ba,wanda ta ce hakan take ‘yancinta ne na fadin albarkacin bakinta.
A kwanakin baya ne majalisar dattawa ta dakatar da Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida, bayan da aka ce ta ‘yi magana ba tare da izini ba’ kuma ta ‘ki amincewa da sabuwar kujerar da aka ware mata a zauren majalisar.
A cikin karar mai lamba FHC/ABJ/CS/498/2025 da aka shigar a ranar Juma’ar da ta gabata a babbar kotun tarayya da ke Abuja, SERAP na neman da a tilasta soke dakatarwar da aka yi wa Natasha Akpoti-Uduaghan ba bisa ka’ida ba, a maido da ita, tare da dawo mata da dukkan hakkokinta.
SERAP na neman Majalisar Dattawa da ta dakatar da daukar duk wani matakin ladabtarwa a kan Natasha Akpoti-Uduaghan.