Wata cuta da ba a kai ga tantance ta ba ta yi ajalin dalibai biya na jami’ar kimiyya da fasaha ta jihar Kebbi dake garin Aleiro.
Magatakardar jami’ar, Maimaru Alhaji Tilli, ta tabbatar da faruwar lamarin.
Wasu daliban jami’ar sun shaida wa gidan talabijin na Channels cewa, mutum hudu sun rasu a makon jiya, yayin da daya ya ce ga garinku nan a jiya Lahadi.
Wata majiya ta ce a makon jiya, jami’an hukumar lafiya ta duniya WHO sun zo domin wayar da kai akan cutar sankarau.