Ma’aunin hauhawar farashi a Nijeriya ya sauka zuwa kashi 23.18 a watan Fabrairu, idan aka kwatanta da kashi 24.48 da ya kai a watan Janairun 2025.
Wannan na kunshe ne a cikin rahoton da hukumar kididdiga ta Nijeriya ta fitar na na Fabrairun 2025.
A cewar ƙididdigar, farashin kayan masarufi ya sauka da kashi 1.30 idan aka kwatanta da watan Janairun wannan shekara.