Kamfanonin dake jigilar masu zuwa umra na fuskantar kalubale wajen samun takardar izinin shiga kasar Saudiyya, lamarin da ya shafi dubban maniyyata.
An dai alakanta wannan matsalar da wani sabon tsari da Saudiyya ta fito da shi, kuma yanzu haka ya sa mutane da dama dake son zuwa kasa mai tsarki sun rasa makoma, kamar yadda kafar Independent Hajj Reporters ta ruwaito.
Sai dai a wata zantawa da mashawarci kan lamurran addini na Saudiyya AFM Khalid Hossain ya ce an dauki matakin ne saboda cunkoson mutanen da ke Saudiyya a yanzu, sun fi na lokacin aikin hajji.