![]() |
| ‘Yan ci rani a Bahar Rum |
Mahukuntan kasar Libya sun mayar da mata da kananan yara sama da 150 zuwa Nijeriya, karkashin wani shiri na “mayar da ‘yan ci rani da ke zaune a kasar ba bisa ka’ida ba” bisa jagorancin Majalisar Dinkin Duniya.
Libya dai ta kasance wurin da yan ci ranin ke haurawa ta gabar tekun Bahar Rum, waɗanda suka fito daga Arewacin Afirka da ke fatan isa Turai.
Majiyoyi daga Hukumar Kula da ‘yan ci rani ta Duniya (IOM), da ke da hannu a shirin mayar da ‘yan bakin hauren, ta ce waɗanda aka mayar din sun hada da mata 160 da kananan yara 17.


.jpeg)

