Babban Lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi, ya ce bai kamata a dora wa ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike alhakin kan ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas.
A ranar Talata ne shugaban kasa Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar saboda rikicin siyasar da ya yi kamari, abinda ya sa wasu ke zargin shugaban da mara baya ga Wike tare da dora laifin rikicin kan Fubara.
Sai dai da yake zantawa da manema labarai fadar shugaban kasa, Lateef Fagbemi ya zargi Fubara da laifin rikicin siyasa ta hanyar roshe harabar majalisar dokokin jihar.