An yi musayar kalamai a zauren majalisar wakilai yayin da wasu ‘yan majalisa mata biyu suka caccaki juna kan dokar ta ɓaci a jihar Ribas.
‘Yar Marie Ebikake daga Bayelsa da Blessing Amadi daga Rivers sun tada jijiyoyin wuya kan damar da kundin tsarin mulki ya bai wa shugaban kasa.
Wasu ‘yan majalisa sun shiga tsakani domin gudun kar a kai ga ba hamatta iska.