Babban bankin Nijeriya CBN ya yi hasashen cewa za a ci gaba da samun saukar farashin kayayyaki cikin watanni shida masu zuwa.
Wannan na kunshe ne a cikin wani rahoto kan hasashen hauhawar farashi na watan Fabrairun 2025 da bankin ya fitar.
A cewar rahoton, ‘yan kasuwa da magidanta su fara shirin ganin saukar farashin kayayyaki cikin watanni shida masu zuwa.