Dakataccen gwamnan jihar Ribas Siminalayi Fubara, ya ce sun karbi dokar ta-bacin da shugaba Bola Tinubu ya kafa cikin lumana da kuma imani da bin tsarin dimokuradiyya.
Ya ce duk da rikicin siyasar jihar, hakan bai shafi harkokin tafiyar da mulki ba.
A ranar Talata ne shugaba Tinubu ya dakatar da Fubara da mataimakinsa da kuma ‘yan majalisar dokokin jihar sannan ya nada wani tsohon hafsan hafsoshin ruwa, Vice Admiral Ibokette Ibas a matsayin gwamnan rikon kwarya na tsawon watanni shida.