Majalisar dokokin jihar Ribas ta nuna amincewar ta da ayyana dokar ta-baci da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin majalisar, Martin Amaewhule ya fitar ranar Talata.
Martin Amaewhule ya ce majalisar za ta yi biyayya ga duk matakan da shugaban kasa ya dauka, duk da cewa ba haka aka so ba.