Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Vice Admiral Ibok-Ete Ibas mai ritaya a matsayin gwamnan rikon kwarya na jihar Ribas.
An yi rantsuwar ne yayin wani kwarya-kwaryar bukin ya gudana da yammacin ranar Laraba a fadar gwamnati da ke Abuja.
Hakan na zuwa ne bayan ganawa da shugaban kasa, da babban lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi SAN da kuma gwamnan rikon kwaryar suka yi.