![]() |
Atiku Abubakar/Peter Obi |
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, tare da na jam’iyyar Labour, Peter Obi, da sauran jiga-jigan ‘yan adawa sun yi kira ga majalisun dokokin kasar da su yi watsi da kakaba dokar ta baci a jihar Rivers da shugaba Bola Tinubu ya yi.
Atiku, wanda ya yi magana a madadin ‘yan adawar a wani taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis, ya zargi Tinubu da nuna son kai da kuma amfani da sashe na 305 da bai dace ba game da sanya dokar ta baci.
Ya yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta soke wannan dakatarwar da yayi da ta sabawa kundin tsarin mulkin kasar, ya maido da zababben gwamna da mataimakiyar sa, da majalisar dokokin jihar Rivers.
Idan dai za a iya tunawa, Jihar Rivers ta kwashe kusan shekaru biyu tana fama da rikice-rikicen siyasance, yayin da tsohon Gwamna Nyesom Wike da magajinsa, Siminayi Fubara ke fafatawa da juna, lamarin da ya janyo cece kuce a jihar.
A dalilin haka ne shugaban ya kakaba dokar ta baci a jihar a ranar Talata.