![]() |
Bello Matawalle |
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a wani jawabi da ya yi a ranar Talata ya kafa dokar ta baci a jihar Rivers tare da dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa Ngozi Odu da ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida sakamakon rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar.
Shugaban ya kuma nada Vice Admiral Ibok-Ette Ibas mai ritaya, a matsayin mai kula da harkokin mulki na jihar na rikon kwarya.
A wata sanarwa da daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar tsaro ya fitar a ranar Talata, ya ce matakin da shugaban kasar ya dauka na da matukar muhimmanci wajen maido da kwanciyar hankali a fagen siyasar jihar.
Ministan ya bayyana cewa sanya dokar ta bacin shine abinda da ya dace don magance rikicin siyasa da ke ci gaba da ruruwa a jihar, wanda ya samu cikas wajen gudanar da mulkin dimokradiyya da kuma jin dadin al’ummar jihar Rivers.
Sai dai shugaban jam’iyyar PDP na jihar Zamfara Jibo Magayaki Jamilu a wata sanarwa da ya fitar jiya ya ce goyon bayan da Bello Matawalle ya bayar kan dakatarwar da aka yi wa Gwamna Siminalayi Fubara ba bisa ka’ida ba ba abin mamaki ba ne, idan aka yi la’akari da irin tarihin da ya yi na tauye ka’idojin dimokaradiyya da ‘yancin dan Adam a lokacin da yake Gwamnan Jihar Zamfara.