DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Zargin nadin mukamai ba bisa ka’ida ba ya kunno kai a hukumar alhazan Nijeriya NAHCON

-

 

Ana zargin shugaban hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya NAHCON Prof. Sale Abdullahi Pakistan da nuna bangaranci a hukumar wajen nada mukamai. Mukamin  Head of Policy and Research na hukumar da aka bai wa wani jami’i shi daga hukumar leken asirin Nijeriya maimakon bai wa ma’aiakcin NAHCOn na cikin gida na cikin misalin da masu korafin ke zargin nuna bangaranci a kansa. Haka kuma suna zargin an sanya mutane masu yawa daga jihar Borno a manyan mukamai na hukumar karkashin jagorancin Prof. Abdullahi Saleh Pakistan. 

Kungiyar manyan ma’aikatan gwamnati ce ke zarginsa da fifita ma’aikatan da aka kawo daga wasu wurare fiye da ma’aikatan da suke na hukumar ne. A cikin wata wasikar korafi da ta aike wa hukumar gudanarwa ta NAHCON, kungiyar ta Association of Senior Civil Servants ta ce idan aka aka ci gaba da tafiya a haka, zargin rashin yi wa ma’aikatan da ke hukumar adalci zai dakushe kwazonsu da hakan na iya shafar ingancin aikinsu.

Kawo yanzu shugabancin hukumar ta NAHCON bai mayar da martani kan wadannan zarge-zargen ba, amma a baya shugaban hukumar Prof. Pakistan ya shaida wa DCL Hausa cewa yana iyakar bakin kokarinsa wajen ganin bai saba wa doka ba a lamarin shugabancin hukumar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An saka ranar da za a fitar da sakamakon binciken zargin alaka da muggan kwayoyi da ya hada da Shugaba Tinubu na Nijeriya

An saka ranar da za a fitar da sakamakon binciken zargin alaka da muggan kwayoyi da ya hada da Shugaba Tinubu na Nijeriya. Ana dai...

Za mu iya cin zabenmu ko babu ku, kalaman Elrufa’i ga gwamnonin Nijeriya

  Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa sabuwar kawancen jam’iyyu adawa na da karfin da zai kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu...

Mafi Shahara