Kotun koli a Nijeriya ta tabbatar da Samuel Anyanwu, kuma na hannun daman ministan birnin tarayya Abuja a matsayin sakataren jam’iyyar PDP na kasa.
Samuel Anyanwu da Sunday Ude Okoye dai sun yi takun-saka tsakaninsu, lamarin da ya janyo rarrabuwar kawuna a tsakanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.
Sai dai Ude Okoye ya samu goyon baya daga bangarori daban-daban na jam’iyyar wadanda suka dogara da hukuncin da wata kotun daukaka kara da ke zamanta a Enugu ta yanke.
Kotun daukaka karar ta tabbatar da tsige Anyanwu da wata babbar kotun tarayya da ke Enugu ta yi.
Sai dai a wani hukunci da aka yanke a ranar Juma’a, kotun mai alkalai biyar, yayin zartar da hukuncin ta ce al’amuran da suka shafi shugabanci a jam’iyyar siyasa al’amari ne na cikin gida, kuma bai kamata ya zama na kotu ba.