![]() |
Rabi’u Musa Kwankwaso |
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi kakkausar suka ga matakin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dauka na kakaba dokar ta baci a jihar Rivers, inda ya ce hakan hadarine ga dimokuradiyyar Nijeriya.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Kwankwaso ya bayyana matukar damuwarsa kan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, da mataimakinsa, da kuma daukacin ‘yan majalisar dokokin jihar da aka zaba, inda ya bayyana matakin a matsayin wuce gona da iri.
Sanata ya yi gargadin a guji maimaita kura-kuran da aka yi a baya, inda ‘yan majalisa suka shagaltu da rigingimun cikin gida maimakon kare tsarin dimokuradiyya.