Shugaban kasar Tunisiya Kais Saied ya sallami Fira ministan kasar Kamel Madouri
Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar a ranar Juma’a.
Kamel Madouri, masanin fasahar kere kere da aka nada a watan Agustan shekarar da ta gabata a matsayin wani bangare na garambawul na majalisar ministoci, an maye gurbinsa da Sarra Zaafrani Zenzri, tsohuwar ministar ayyuka inji fadar shugaban kasar.
Zaafrani, mai shekaru 62, ta zama mace ta biyu a matsayin Firaminista a Tunisia bayan Najla Bouden, wacce ta samu mukamin daga Oktoba 2021 zuwa Agusta 2023.
Ta hau karagar mulki yayin da Tunisia ke fuskantar suka daga Majalisar Dinkin Duniya kan daure ‘yan adawar siyasa Saied da kuma yadda kungiyoyin kare hakkin bil adama ke yin Allah wadai da koma bayan ‘yancin dan adam a kasar.