![]() |
Farfesa Abdullahi Sale Usman |
Kungiyar Progressive Northern Youth PNY, ta musanta zargin nuna son kai da kuma rashin adalci da ake yi wa shugaban hukumar alhazai ta Nijeriya NAHCON, Farfesa Abdullahi Sale Usman.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Ko’odinetan kungiyar Dr, Muktar Suleiman,ya bayyana zargin a matsayin mara tushe, yana mai cewa wannan aikin ‘yan zagon kasa ne, wadanda suke son su kawar da hankalin hukumar daga aikinta.
A cewarsa, wasu mutanen da ba su ji dadin nasarorin da hukumar ta samu a karkashin jagorancin Farfesa Usman, suna aiki tukuru don ganin sun tozarta sunansa da na gwamnatin Tinubu.
Suleiman ya kara da cewa, kwararan hujjoji sun tabbatar da cewa babu manyan jami’an hukumar ko shugabanninta da ke yin katsalandan ga ka’idojin da aka gindaya da ke jagorantar ayyukan hukumar.
Ya bukaci ‘yan Nijeriya masu kishin kasa da su rika samun sahihin bayanai daga hukumar kafin su je ga manema labarai.